An Bukaci Gwamnatin Kaduna Da Ta Janye Dokar Hana Sallar Juma’a

0
998

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

A KOKARIN da gwamnatin Jihar Kaduna take yi don hana kara yaduwar Cutar Korona ta hanyar hana duk wasu tarurruka na cunkoso, an bukatar gwamnatin Jihar Kaduna da ta sassauta dokar hana yin sallar Juma’a don neman yin addu’o’i  neman mafita wajen Ubangiji a kan wannan cutar da ta addabi duniya baki daya.

Kungiyar Fityanul Islam na kasa ne ta bayyana hakan a shafinta na sada zumunta a wani sakon da ke da sa hannun Mataimakin shugaban kungiyar Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zariya.

Sheikh Khalifa ya bayyana cewa lallai akwai matuka bukatar a duba maganar dokar dakatar da sallar Juma’ar domin tsakani da Allah babu wata hujja na barin sallar Juma’ar idan har fargabar kamuwa da cutar ba ta hana zuwa kasuwanci ba.

Ya ce ” Ya zama dole ne mu fito mu fada wa kanmu gaskiya, idan har gwamnati za ta iya ba jama’a damar fitowa kasuwanci cikin cunkoso don neman abinci a ranakun Talata da Laraba ba tare da fargabar yaduwar cutar Korona ba, toh lallai akwai bukatar a duba maganar dokar sallar Juma’a.”

Ya kara da cewa ya kamata gwamnatin jihar da ta duba wannan lamarin kuma ta yi koyi da sauran jihohin Arewa kamar Sakkwato, Kano, Bauchi da Filato wadanda suka samar da ko’idoji da tsarin da za a bi don kauce wa yaduwar cutar a lokacin gudanar da sallar Juma’ar maimakon dakatar da ita.

A cewarsa, lokacin sallar ba ta wuce awa daya zuwa biyu ya isa a gudanar da sallar Juma’ar wanda kuma wajibi ne a nan za a roki Ubangiji don neman tsari da kariya daga kara yaduwar Cutar a cikin al’umma da kasa baki daya.

A karshe, sakon ya yi kira ga gwamnatin jihar ta Kaduna da tattausar murya da ta dubi Allah ta dauke wannan dokar ta hana sallar Juma’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here