An Tabka Wawaso Yayin Rabon Tallafin Kayan Abincin Gwamnatin Kaduna

0
400

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

WASU al’umna mazauna unguwar Narayi da gundumar Rigasa da ke garin Kaduna sun yi wawason kayan abincin da aka ajiye da niyyar raba wa marasa karfi a unguwa yayin da ‘yan kwamitin da aka daura wa alhakin rabon kayan abincin suka zuba musu ido suna kallonsu babu yadda za su yi da su.

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da kayayyakin abincin ne domin a raba wa talakawa yayin da suke zaune a gidajensu sakamakon dokar hana fita da aka saka saboda cutar coronavirus.

Shugaban kwamitin rabon, Malam Sule Garba ya ce lamarin ya afku ne a ranar Litinin da yamma a makarantar firamari ta LEA da ke Narayi.

Garba wanda kuma shi ne mai unguwar ta Narayi, a ranar Talata ya bayyana cewa dandazon mata sa maza da mata sun suke wawushe kayin abincin suka tsere.

Ya lissafa cewa kayayyakin sun kunshi katon 170 na taliyar spagetti, katon din Indomie 1,250, kananan jakunkuna da aka dauke da shinkafa mudu 650, wake mudu 230 da galan din man gyada 800.

Ya yi bayanin cewa saboda adalci da gudun zargi, kwamitin da sauke kayayyakin ne a makarantan LEA na Narayi jim kadan sai mata da yara suka cika wurin domin karbar rabon su.

Ya ce an fara samun matsala ne lokacin da yan kwamitin suka gaza cimma matsaya kan tsarin da za ayi amfani da shi wurin rabon kayan tallafin.

Mai unguwar ya ce ana cikin wannan hali ne sai wasu mutane suka fara daukan kayan abincin suna mika wa yan gidansu da abokansu.

Ya ce, “Muna cikin rabon kayan abincin daya bayan daya kwatsam sai mutanen suka fi karfin mu, kowa ya fara diban abinda hannunsa zai iya dauka.

“Mun yi iya kokarin mu amma sun mana yawa domin kowa cikin su yana son ya samu rabonsa ne ta ko wane hali.”

Ya kara da cewa mambobin Kungiyar Civilian JTF da ya kamata su ba su tsaro su kuma taimaka wurin tabbatar da cewa mutanen sun bi tsari su ma suka shiga wawason domin samun rabonsu. Garba ya ce, “Na gode wa Allah tun da babu wanda ya rasa ransa.”

Da ya ke martani kan lamarin, shugaban Civilian JTF, Mista Silas Kuje ya ce bai da labarin cewa yan kungiyarsa sun shiga warwason amma ya ce zai yi bincike a kan zargin.

Hakazalika a gundumar Rigasa, rahotanni sun bayyana cewa, an samu batan motoci biyu tun daga wajen kawo kayan abincin, kana wasu matasa sun kwace wasu kayayyakin abincin a kan hanya kamin a karasa da su wajen da za ayi rabon.

Bugu da kari, mafi akasarin al’ummar da aka je da kayan abincin don raba musu basu samu ba sakamakon karancin da kayan abincin suka yi, kana da nuna halin sonrai da wasu daga cikin masu rabon kayayyakin suka yi bayaga dauki daya-daya da wasu matasa yi ta hanyar zarewa musu rabon makamai da rotsa motocin wasu daga cikin su dukda yake ba asarar rai illa cin mutunci da zarafi da aka yiwa wasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here