Isah Ahmed Daga Jos
MAWAKIN siyasar nan da ke zaune a garin Kano, Nazifi Sharif ya daga taron raba kyaututtukan gasar wakarsa, ta ‘’Hanta da Jini’’ da ya yi wa Sanatan mazabar Kaduna ta tsakiya Sanata Uba Sani da ya sanya, saboda halin da ake ciki na bullar cutar annobar korona, har sai al’amura sun daidaita.
Tun da farko dai mawakin ya shirya zai gudanar da taron raba kyaututtuka da suka hada da mota da keke Napep da babur da kudade ga wadanda suka zamo zakaru a gasar ne, a ranar Lahadin nan a garin Kaduna.
Da yake zantawa da wakilinmu kan daga wannan taro, Mawaki Nazifi Sharif ya bayyana cewa abin da ya sa suka daga wannan taro, shi ne saboda halin da duniya ta shiga na annobar korona.
Ya ce ada sun shirya cewa za a rufe karbar wannan gasar ce, a ranar 30 ga watan nan da ya gabata. Sannan alkalan gasar su duba wadanda suka ya yi nasara, tun daga na daya har ya zuwa na 10. Kuma a ba su kyaututtukan a wannan taro, da aka daga.
Ya ce an shirya cewa wannan taro zai sami halartar gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufa’i da Sanata Uba Sani da shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawal da sauran manyan baki daga jihohi.
Ya ce saboda wannan hali da aka shiga na wannan annoba ta cutar korona suka dage taron, har sai abubuwa sun dai dai ta, kan wannan hali da ake ciki. Daga baya idan an sami saukin wannan annoba, a sake sa ranar taron.
‘’Tun da an daga wannan taro zamu sake bude kofa ga wadanda ba su sami damar shiga wannan gasa ba, domin su sami damar shiga. Ya zuwa yanzu dai, mutanen da suka shiga wannan gasa, maza da mata sun kai 830’’.