Buhari Ya Gargadi Sojoji Da Su Kauce Wa Cin Zarafin Yan Najeriya Kan Dokar Ta-Baci

0
284

Daga Usman Nasidi.

SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya gargadi jami’an hukumomin tsaro da aka jibge su domin tabbatar da dabbaka dokar hana shige da fice a jahohin Najeriya da su daina cin zarafin jama’a tare da kuntata musu.

Sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Mustapha kuma shugaban kwamitin shugaban kasa na ko-ta-kwana a kan Coronavirus ne ya bayyana haka yayin da yake bayar da jawabin ayyukansu a ranar Juma’a, a Abuja.

Buhari ya gargadi Sojoji da su kauce ma cin zarafin yan Najeriya saboda dokar ta-baci
Boss ya yi kira ga yan Najeriya su kasance masu bin doka da oda, tare da kasancewa masu hakuri da kuma kiyayewa. “Sakon shugaban kasa shi ne kada wani dan Najeriya ya cutu a sanadiyyar dokar ta baci da aka sanya.

“Muna samun rahotanni masu faranta rai dake nuna jama’a na bin umarnin zaman gida a Legas, Ogun da babban birnin tarayya Abuja.

Cutar COVID-19 fitina ne ga duniya gaba daya, kuma tana barazana ga tsaron kasarmu da tattalin arzikinmu, don haka ya kamata kowa ya taka rawarsa don kawo karshen aikin.

“Ga yan kasuwa maza da mata, muna kira su daina tsawwala farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi, kamata yayi mu kasance masu tausayin juna da sassauci a wannan lokaci, wannan ne lokacin da ya fi kamata mu nuna fahimtar juna.

“Duba da hadarin da ma’aikatan kiwon lafiyanmu suke ciki musamman wadanda ke kula da masu cutar, gwamnati na aiki da masu ruwa da tsaki don samar da inshoran lafiya da inshoran rayuwa gare su, don haka nake basu tabbacin kulawar gwamnati, kuma su masu dage wajen ceton rayukan jama’a.” Inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here