COVID-19: Hukumar SEMA A Yobe Ta Rarraba Wa Nakasassu Kayayyakin Abinci

0
392
Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu
HUKUMAR bayar da agajin gaggawa (SEMA) ta Jihar Yobe ta gudanar da aikin rarraba wa nakasassu kayan abinci kyauta, don saukaka musu matsin rayuwa a lokacin da su ke zaune a gida sakamakon  takunkumin hana walwala saboda hana ci gaba da yaduwar annobar Covid-19 da gwamnatin jihar tasa .
Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin Sakataren hukumar SEMA a jihar Yobe, Dokta Muhammed Goje, a lokacin da ya ke jagorantar raba kayan abincin a daya cibiyar raba kayayyakin, a birnin Damaturu fadar gwannatin jihar.
Sakatareb hukumar ta SEMA ya kara da bayyana cewa, gwamnatin jihar ta zabi bayar da muhimanci wajen raba kayan abincin ga wannan bangare na nakasassun, saboda yadda su ne al’ummar da su ka fi kowa rauni kuma wadanda kwayar za ta fi yi wa lahani ba tare da jinkiri ba.
A cewarsa  a duk lokacin da ka shawarci jama’a da cewa su zauna a gida, ya hada har da nakasassu a ciki, wadanda a zahiri su ne ke dauke da wata lalura a rayuwa wadda in ba haka ka musu ba to akwai matsala.
Ya kara da cewa wadannan jama’a su ne ke fita waje su na bi lungu-lungu su na bara a
kan tituna, wadanda kuma su ne ke mu’amala da jama’a kai-tsaye daban-daban, a tasha ko masu wucewa zuwa wasu garuruwa a jihar baki data.
“Yayin da ake basu sadakar kudi ko su hada hannu da jama’a, wanda wannan daya ne daga cikin manyan hanyoyin da ake kamuwa da wannan hattsabibiyar kwayar cuta ta Covid-19 kai tsaye.
Sakataren hukumar ta SEMA, ya kara da cewa, yana daga cikin kyawawan kudurorin gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni, shi ne kyautata jin dadin su tare da daukar matakin bibiyar su gida-gida ana basu tallafi.

Wasu daga cikin kayayyakin  abinci da aka rarraba, sun kunshi shinkafa, wake, masara, gishiri, man girki da makamantan su.

A nasa jawabin a madadin wadanda su ka ci gajiyar tallafin, shugaban kungiyar a arewa maso gabas, Muhammed Isah, ya yaba matuka da kayan
tallafin, wanda gwamnatin jihar ta bayar.

A cewarsa, ba wannan ne karon farko ko na biyu ba, wanda gwamnatin Mai Mala ta yi irin wannan taimakon ga jama’a masu dauke da lalura ba. Sannan kuma wannan na musaman ne wanda an yi shi ne don rage wa jama’ar mu
mawuyacin halin da suke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here