Gwamnatin Kaduna Ta Gurfanar Da Fastoci 2 Gaban Kotu Kan Karya Umurnin Gwamna

0
348

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GWAMNATIN jahar Kaduna ta sanar da kama wasu limaman coci-coci guda biyu tare da gurfanar da su gaban wata kotun majistri sakamakon kama su da ta yi da tara gangamin jama’a a cocinsu a ranar Lahadin da ta gabata.

Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jahar, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka, inda ya ce an kama Fastocin ne a unguwar Sabon Tasha da ke cikin karamar hukumar Chikun, inda suke keta umarnin gwamnan jahar na hana duk wasu taruka saboda gudun yaduwar Coronavirus.

Aruwan ya bayyana sunayen Fastocin kamar haka; Fasto Ifeanyi Ojonu da Fasto Giniki Okafor, wanda ya ce an gurfanar da su gaban kotu a kan tuhumarsu da laifuka biyu da suka hada da hadin baki da kuma kin biyayya ga halastaccen umurni bisa sashi na 59 da 115 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Kaduna.

Aruwan ya kara da cewa an samu matsalolin rashin biyayya ga umurnin gwamnati na killace kai tare da kula da duk wasu hanyoyin kare kai daga kamuwa daga cutar Coronavirus, hakazalika ababen hawa na haya na ci gaba da aiki a garin Kaduna, wanda hakan ta sa gwamnati ta yi barazanar dakatar da sassauta dokar da ta yi niyya.

“Mun samu goyon baya da hadin kan kungiyoyin Musulunci, duka da yadda suka garkame Masallatansu na sallolin yau da kullum, da ma Masallatan Juma’a, hakazalika an rufe cocina da dama, amma akwai wasu limamai biyu da suka shirya sallar juma’a a ranar 27 ga watan Maris.

“Ba tare da wata wata ba aka kama su, kuma aka gurfanar da su gaban kuliya manta sabo a ranar 30 ga watan Maris, da wannan gwamnati ta nanata cewa babu wanda ya fi karfin doka, don haka zamu dabbaka dokar hana zirga zirga ba tare da tsoro ko son kai ba.” Inji shi.

Daga karshe Aruwan ya yi kira ga jama’ar jahar Kaduna su tabbata sun kai karar duk wani jami’in gwamnatin jahar Kaduna ko kuma jami’in tsaro da ya ci zarafinsu ko kuma ya tauye musu hakkokinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here