Hukumar Kwastan Ta Saki Tireloli 247 Dankare Da Kayan Abinci Da Ya Kai Naira Biliyan 3.2

0
387

Daga Usman Nasidi.

SHUGABAN hukumar kwastan na Najeriya, Kanar Hameed Ali, ya amince da sakin manyan tireloli 247 cike da kayan tallafi, wanda farashin su ya kai naira biliyan 3.250 a kasuwa sannan harajinsu ya kai naira biliyan 2 daga dakin ajiyarsu.

A wata sanarwa daga jami’in hulda da jama’a na hukumar kwastam, Joseph Attah, ya ce hakan na daidai da umurnin da shugaban kasa ya bayar na cewar a raba kayan da hukumar kwastam ta kwace ga al’umman kasar.

Ya ce an dauki wannan mataki ne sakamakon ci gaba da tsare mutane da aka yi a gida domin hana yaduwar cutar Coronavirus a kasar.

Jawabin ya kuma bayyana cewa a martani game da radadin da ke tattare da hana mutane walwala a wasu yankunan kasar, wasu yan Najeriya sun nemi hukumar kwastam da ta raba shinkafa da sauran kayan amfani da ta kwace ga jama’a.

Kayayyakin sun hada da tirelar shinkafa 158 wanda aka kiyasta a tan 46,000, tirela 30 na man gyada mai lita 25 guda 36,495, da kuma jarkan man ja guda 3,428.

Sauran sun hada da tireloli 54 da ke dauke da katan din timatirin gwangwani 136,705, katan din taliya guda 2,951 da pakitin noodles 1,253, sinkin atamfofi 828 da kuma leshi 2,300.

Za a kwashi dukka kayayyakin ne a tireloli 247, domin hukumar kwastam ta ce kayan da zai dace da cin mutane kawai za a sakarwa mutane.

A daidai lokacin kawo wannan rahoton ba a bayyana wurin da za raba kayayyakin ba tukuna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here