Sheikh Jingir Ya Bi Umurnin Lalong, Ya Yi Sallar Juma’a A Gida

0
444

Daga Usman Nasidi.

SHUGABAN kungiyar musulunci ta Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’Ikamatis Sunnah, JIBWIS, a jihar Filato, Sheikh Sani Jingir, daga karshe ya yi biyaya ga dokar Gwamna Simon Lalong na hana duk wata taro na sama da mutane 50 a jihar domin kare yaduwar cutar coronavirus.

Idan ba a manta ba, Sheikh Jingir ya yi wa daruruwan mutane limancin sallar Juma’a a masallacinsa na ‘Yan-taya a makon da ta gabata a ranar 27 ga watan Maris duk da dokar da gwamnatin jihar ta saka.

Daga bisani, hukumar ‘yan sandan farin kayan SSS sun gayyace shi ofishinsu game da saba dokar da ya yi na gwamnatin jihar a wannan lokacin da ake kokarin dakile yaduwar cutar.

Yayin amsa tambayoyin a ofishin DSS , an ruwaito cewa an tilasta wa Sheikh Jingir rubuta takardar rantsuwa ta jaddada mubaya’arsa ga gwamnatin jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa ba a ga Sheikh Jingir ba a harabar masallacin a lokacin sallar Juma’a inda wasu masallata da suka yi sallar su a masallacin na ‘Yantaya.

Wata majiyar ta bayyana cewa ya yi sallarsa ne a masallacin gidansa tare da mutane kalilan kamar yadda hotunan ke nunawa.

A baya-bayan nan dai Sheikh Jingir ya janyo cece-kuce tsakanin mutane saboda kin biyaya ga dokar gwamnatin da kuma ikirarin da yake yi na cewa bai amince akwai cutar coronavirus ba.

An ruwaito cewa Sheikh Jingir ya yi ikirarin cewa bullar annobar ta coronavirus ba komai ba ne illa sharri da makirci na Yahudawa da ke kokarin dakile musulunci da musulmi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here