‘Yan Abuja Sun Koka Kan Yadda Ake Gudunsu Saboda Cutar Korona

0
353

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

WASU jama’a na gudun mutanen da suka dawo jahar Adamawa daga Abuja da Lagas kan tsoron kamuwa da cutar covid-19 wacce aka fi sani da coronavirus.

Jahar Legas da babbar birnin tarayya Abuja su ne ka wajen yawan mutanen da suka kamu da COVID-19 yayin da gwamnati ke fafutukar ganin ta hana yaduwar cutar.

Ali Kaka, wani abokin Mohammed Atiku, dan tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda ya kamu da cutar a kwanakin da suka gabata, ya ce ya cika da mamaki a lokacin da wasu tawagar abokansa suka tarwatse a lokacin da ya doshe su ‘yan kwanaki bayan ya dawo daga Abuja.

Ya ce an yada jita-jita a fadin Yola cewa ya hadu da Muhammed Atiku a Abuja, wanda hakan ya sa mutane ke gudun hada inuwa dashi.

“Wallahi, ban hadu da Muhammed ba a Abuja ko kadan. Ganinmu na karshe da shi tsawon watanni uku da suka gabata ne kuma a nan Yola ne, amma wasu mutane sun yada jita-jita domin batar da jama’a.

“Tabbass, Muhammed Atiku abokina ne amma bamu hadu dashi ba a zuwan da na yi Abuja na karshe. Da a ce mun hadu da shi, zan nemi a gwada ni saboda ina so na kasance cikin koshin lafiya,” in ji shi.

Kan haka, Kaka ya sha alwashin daukar matakin
doka idan ya gano tushen jita-jitan domin ya zama darasi ga masu tsegumin.

Wasu daga cikin abokan Kaka sun ce da fari sun yarda da jita-jitan sannan suka kaurace masa saboda sun ji cewa ya halarci wani taro tare da Atiku Abubakar, sannan cewa ba za su iya wargi da lafiyarsu ba.

Wani mutum kuma da ya dawo daga Abuja, Musa Ine, ya yi korafi kan yadda makwabta da abokansa suka dunga yi masa, cewa mutane na ta kaurace masa tare da gulma a kansa ba tare da wani dalili ba.

“Sai na gano wani rade-radi da ke yawo, cewa na hadu da wasu manyan mutane a Abuja wadanda suka riga suka kamu, don haka mutane suka ki zuwa kusa da ni. Na je waji shago sayan abubuwa, sai wani abokina ya yi gaggawar barin shagon ba tare da ya yi mun magana ba,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here