Yayan Gwamnan Jahar Bauchi Ya Fito Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane

0
395

Daga Usman Nasidi.

YAYAN Gwamnan jahar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, wato Yaya Adamu ya kubuta daga hannun miyagun ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane bayan kwashe kwanaki 12 a hannunsu.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jahar, DSP Kamal Abubakar ne ya bayyana haka ga manema labaru da daddaren Talata, 7 ga watan Afrilu, inda ya ce: “Game da tuntubar da kuka yi a kan wannan magana, ina tabbatar da muku da cewa wanda aka sacen ya samu yancinsa, kuma a yanzu haka ya koma wajen iyalansa a yau 7 ga watan Afrilu na shekarar 2020.” Inji shi.

Mai magana da yawun ‘yan sandan bai bayyana ko an biya kudin fansa kafina sako Yaya Adamu ba, ko kuwa a’a.

Idan za a tuna ba’a gama jimamin kamuwar gwamnan Bauchi, Bala Muhammad da annobar Coronavirus ba, kwatsam sai aka wasu gungun miyagu yan bindiga suka sace Yayansa, Yaya Adamu.

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da Yaya Adamu ne a ranar Laraba, 25 g watan Maris da misalin karfe 7:30 na dare a gidansa da ke Unguwar Jaki, cikin kwaryar garin Bauchi.

Wannan lamari ya faru ne bayan kimanin sa’o’i 72 da Gwamnan jahar Bauchi, Bala Muhammad ya killace kansa daga cudanya da jama’a sakamakon mu’amalar da ya yi da wani mutumi da ke dauke da cutar Coronavirus.

Daga bisani a ranar Talata aka tabbatar da Gwamnan ya kamu da cutar, bayan sakamakon gwajin da jami’an hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC, suka gudanar a kansa ya tabbatar da hakan.

Babban hadimin Gwamnan a kan harkokin watsa labaru, Mukhtar Gidado ne ya tabbatar da aukuwar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here