Korona Bairos: ‘Yan kabilar Igbo Sun Bai Wa Gwamnatin Kano Tallafin Kayan Miliyan 5

0
667

Rahoton Z A Sada

SHUGABAN Kwamitin tattara tallafin Coronavirus da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa wato Farfesa Muhammad Yahuza Bello tare da ‘yan kwamitinsa sun karbi kayan tallafi daga kungiyar masu sayar da magunguna na kabilar Igbo domin a tallafa wa mabukata.

Kayayyakin sun hada da:

1. Indomie katan 100

2. Man goge hannu da ke yajar kwayoyin cuta (Hand sanitizer) mai mililita 500, guda 120

3. Katan din sabulu biyar 75

4. Fakitin safar hannu 70

5. Buhun shinkafa 100

6. Katan din Macaroni 50

Jumullar kudin kayayyakin ya kai kimanin naira miliyan 5.1.

Gudunmowar kabilar Ibo a Kano
Gudunmowar kabilar Ibo a Kano
Gudunmowar kabilar Ibo a Kano
Gudunmowar kabilar Ibo a Kano

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here