Masallacin Sultan Bello Ya Tallafa Wa Gidaje 150 Da Kayayyakin Abinci

0
448

Isah Ahmed Daga Jos

GANIN irin matsanancin halin da al’umma suka shiga na zaman gida, sakamakon dokar hana fitar da gwamnatocin Najeriya suka sanya, don gujewa yaduwar cutar annobar korona, Masallacin Sultan Bello da ke garin Kaduna ya tallafa wa gidaje 150 da kayayyakin abinci da suka hada da shankafa  da gyero da fulawa da taliya da man gyada, tare da tallafin kudade ga tsofaffi da malaman masallacin mutum 110, domin sassauta masu hali da aka shiga.

Da yake zantawa da wakilinmu kan wannan tallafi da masallacin ya bayar, Babban Limamin masallacin Sheikh Muhammad Sulaiman Abu Sulaiman ya bayyana cewa, ganin irin tsananin da ake ciki yanzu, sakamakon annobar cutar korona, ya karfafa wa masallacin gwiwar bayar da wannan tallafi.

Ya ce  kayayyakin abincin da suka  saya   suka raba, sun  hada da shinkafa da gyero da fulawa da taliya da man gyada na gidaje  guda 150,  suka raba wa masu gidajen, don a rage masu halin radadin da ake ciki na zaman gida.

Ya ce baya ga wannan tallafin kayayyakin abinci na  gidaje guda 150,  kuma sun bayar da   tallafin kudade ga tsofaffi da malamai  na masallacin da kuma iyalan wasu malamai da suka rasu mutum 110.

Har’ila yau ya ce ganin wannan abu da masallacin ya yi, ya sanya  wasu mutane suka kawo nasu gudunmawar, suka ce a raba wa mutane.

Ya ce wannan aiki na tallafa wa jama’a a wannan hali da muke ciki,  aiki ne na lada don haka, ya kamata kowa ya fito ya tallafa, ba wai sai gwamnati kadai ba.

Ya yi kira ga al’ummar musulmi da suka yi niyar tafiya umra a bana, su yi amfani da kudaden umrar wajen sayen kayayakin abinci don su raba wa marayu da fakirai a watan Azumi mai zuwa,  ganin  bana babu tafiya aikin umra.

‘’A bana babu umra saboda haka kudaden da masu hali za su yi amfani da su wajen tafiya aikin umra, su yi amfani da su wajen ciyar da al’umma, a lokacin watan Azumin Ramadan, ta hanyar sayen kayayyakin abinci su raba wa marayu da fakirai  a lokacin watan Azumi. Yin haka kamar yin aikin umrar ne’’.

Ya yi  kira ga gwamnatin tarayya da  gwamnatocin jihohi su dauki matakin da gwamnatocin da wasu kasashen duniya suka dauka, na dauke wa talakawansu biyan kudaden ruwa da wutar lantarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here