Masari Ya Ba Da Umurnin Ci Gaba Da Yin Sallar Juma’a

0
290
Mustapha Imrana Abdullahi
GWAMNATIN Jihar Katsina ta sassauta dokar hana zuwa Sallar Juma’a wadda za a ci gaba daga wannan satin akan wasu tsare-tsare da dokoki da tayi kamar haka:
1. Ba da dama ga wasu Manyan Masallatai tare da samar masu abubuwan kariya irinsu: i. Tankunan ruwa ii. Sabullai iii. Abin kariyar hanci da baki (face mask)
2. Takaita Hudubobi da Sallah domin sallamar al’uma cikin lokaci
3. An ba da dama ga duk wani Masallacin Juma’a yin Sallah matukar zai tanaji duk irin abubuwan da gwamnati ta tanada a Masallatan da taba damar yin Sallar.
Muna rokon Allah ya kara tsaremu daga wannan annoba inda kuma ta shiga Allah ya yaye masu ita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here