Annobar Korona: Gwamnatin Filato Ta Kafa Kotunan Hukunta Masu Karya Dokar Hana Fita

0
344

Isah Ahmed Daga Jos

A yayin da gwamnatin jihar Filato ta kafa dokar hana fita a dukkan fadin jihar, wadda ta fara aiki a daren ranar alhamin din nan. Gwamnatin ta  kafa kotunan tafi da gidanka na musamman  guda 10, don hukumta dukkan  wadanda suka karya wannan doka. Wata sanarwar da ta fito da ke dauke da sanya hanun kwamishinan watsa labaran jihar, Mista Dan Manjang ce ta bayyana haka.

Sanarwar ta yi bayanin cewa an kafa wadannan kotuna ne don ganin an tabbatar  al’ummar jihar, sun yi biyayya ga wannan doka, da aka kafa don kare yaduwar  annobar  korona a jihar. Don haka sanarwar ta shawarci al’ummar jihar su yi biyayya da  wannan doka, ta hanyar zama a gida.

Tun da farko dai gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta kafa dokar hana fita tare da rufe jihar ga baki ne, don ganin ta kare annobar korona shiga cikin jihar, har na tsawon mako guda.

Gwamnatin ta yi bayanin cewa a yayin wannan rufe jihar da aka yi, tare da hana fitar jama’a. Za a yi feshin magungunan kashe cututtuka a garin Jos da kewaye, da dukkan kananan hukumomin jihar 17.

Har’ila yau gwamnatin ta ce a yayin wannan zaman gida, wadanda za a bari su ci gaba da zirga-zarga su ne jami’an tsaro da ma’aikatan kiwon lafiya da ‘yan jarida da masu gidajen mai da ma’aikatan kashe gobara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here