Buhari Ya Gana Da Kwamitin Ko Ta-Kwana A Kan Annobar Covid-19

0
296
Daga Usman Nasidi.
A jiya ranar Juma’a ne, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gana da kwamitin ‘ko ta kwana’ da ya kafa a kan annobar cutar covid-19.
A cikin wata sanarwa da shugaba Buhari da kansa ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya bayyana cewa ya na matukar godiya ga kwamitin bisa jajircewarsa a kan aikin da aka dora masa.
Kazalika, ya nuna karfin gwuiwarsa a kan cewa kokarin da kwamitin ya ke yi, zai bawa Najeriya damar samun nasara a kan wannan annoba.
“A yau ne kwamitin ko ta kwana a kan shawo kan annobar cutar covid-19 ya kawo min ziyara domin yi min bayani a kan aiyukansu da halin da ake ciki.
“Ina mai farin ciki da godiya bisa jajircewarsu wajen sauke nauyin da aka dora musu. Ba ni da kokonto ko kadan a kan cewa kokarinsu zai bai wa Najeriya damar samun nasara a kan annobar ,” a cewar Buhari.
Shugaba Buhari ne ya kafa kwamitin na ‘ko ta kwana’ a karkashin jagorancin ministan lafiya, Dakta Osagie Enahire, bayan bullowar annobar cutar covid-19.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here