Mutane 305 Ne Ke Dauke Da Cutar Korona A Nijeriya

0
416
Mustapha Imrana Abdullahi Da Z A Sada
A sababbin alkalumman da hukumar yaki da hana yaduwar cututtuka ta Nijeriya (NCDC) ta fitar sun bayyana cewa a halin yanzu akwai mutane 305 da suke dauke da cutar a tarayyar Nijeriya baki daya.
Hukumar ta bayyana cewa faruwar hakan ya biyo bayan irin yadda aka samu mutane 17 ne da suka kamu da cutar a jihohi daban-daban da suka hada da Kaduna, Katsina, Abuja da sauransu.
Hukumar dai na kara yin kira ga daukacin jama’a da su ci gaba da kiyayewa da matakan hana yaduwar cutar a tsakanin jama’a da suka hada da wanke hannu a kai a kai akalla duk bayan mintuna 30 kiyayewa da masu yin atishawa, tari da kuma yawan taba idanu ko hanci da hannu ga mutum da kuma daina shiga ko zama a cikin cinkoson jama’a.
A cikin wannan adadin mutane 17 da aka samu sun kamu akwai daya a Kaduna da 3 daga Jihar Katsina da suka kasance iyalan Likitan da ya mutu ne a garin Daura sakamakon cutar inda matarsa da ‘ya’yansa biyu duk aka same su sun kamu da cutar Covid – 19 da ake cewa korona bairos.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here