Sakamakon Gwajin Lalong Da Iyalansa Ya Nuna Ba Sa Dauke Da Cutar Korona

0
399

Isah Ahmed Daga Jos

SAKAMAKON gwajin da hukumar kare yaduwar cututtuka ta kasa NCDC,  ta yi wa Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong da iyalansa, a dakin bincikenta da ke Abuja, ya nuna cewa Gwamnan da iyalansa ba sa dauke da wannan cuta. Sakamakon binciken ya fito ne a ranar Alhamis.

Da yake magana  kan wannan al’amari gwamna Lalong, ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki na yin wannan gwaji tare da iyalansa ne, don  ganin an taimaka wajen kare yaduwar wannan cutar annoba ta Kurona.

‘’Wannan cuta ta korona, ba  cuta ce da mutum zai ce don ya kamu da ita, shi ke nan ya mutum ba. Idan ba mu natsu ba, za mu riqa mutuwa saboda tsoro don mun kamu wannan cuta. Don haka muna kira ga al’ummar jihar Filato su fito su yi gwajin wannan cuta, musamman wadanda suka ga alamun wannan cuta tattare da su’’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here