Ko Najeriya Na Da Dalilin Ci Gaba Da Karbar Kudin Aikin Hajjin 2020?

0
491

 Rahoton Z A Sada

Dakin Ka'aba
Saudiyya ta shawarci kasashe su dakata da karbar kudin alhazai ne saboda annobar Korona Bairos

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya ta ce har yanzu ana ci gaba da karbar kudin aikin Hajjin bana, duk da yake mahukuntan Saudiyya sun ba da shawarar a dakata tukuna.

Sai dai hukumar ta ce kananan shirye-shirye ne take yi, wadanda ba su shafi kulla yarjejeniya da wasu kamfanoni ba.

A hirarsa da Sashen Hausa na BBC, kwamishinan ayyuka a hukumar Abdullahi Hardawa ya fada wa Umar Mikail cewa shirin “na ko-ta-kwana” ne.

A farkon watan Afrilu ne Saudiyya ta nemi kasashen duniya su dakatar da karbar kudaden jama’a domin zuwa aikin Hajjin bana saboda annobar coronavirus.

Ministan aikin Hajji Mohammed Banten ya ce Saudiyya ta damu da lafiyar Mahajjata sannan ya yi kira ga jama’a su “jira kafin su biya kudin”.

Sai dai Abdullahi Hardawa ya ce shirin da suke yi bai shafi kulla yarjejeniya da wasu kamfanoni ba da suke yi wa alhazzai hidima a Najeriya da kuma Saudiyya ba.

“Ai dama ba cewa aka yi ba za a yi Hajji ba, saboda haka za mu iya ci gaba da kananan shirye-shirye, duk lokacin da Allah ya sa annobar ta wuce mu ba za mu samu matsala mai yawa ba,” in ji shi.

Ya kara da cewa: “Mahajjata suna bai wa hukumomin jihohi kudinsu sannan a yi musu rajista kuma ba za mu katse musu hanzari ba.”

Kazalika ya ce da yawan mahajjatan ba lokaci guda suke biyan kudin ba, saboda idan lokaci ya kure ba za su iya biya ba.

“Idan Allah ya kaddara ba za a yi Hajji ba to za a mayar wa masu bukata kudinsu,” a cewarsa.

Ya kara cewa da ma ba sabon abu ba ne wasu su bukaci a mayar musu da kudinsu, wasu kuma kan bari sai shekara ta gaba sai su karbi kujerar.

Ana sa ran fiye da Mahajjata miliyan biyu ne za su tafi Makkah da Madina a watan Yuli zuwa Agusta domin gudanar da aikin Hajji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here