Ya Roki ‘Yan Najeriya Da Su Mutunta Umurnin Zama A Gida

0
329

Rahoton Z A Sada

SHUGABA Muhammadu Buhari ya yi kira da babbar murya ga ‘yan kasar su ci gaba da mutunta umurnin zama a gida ba tare da fita ba domin a yaki cutar.

Mai magana da yawun shugaban Najeriyar, Garba Shehu ya ce Buhari ya kuma gode wa al’umma bisa hakuri da suka yi, da kuma kwarin gwiwar da suke bayarwa wajen yaki da barkewar cutar covid-19.

Ya ambato shugaban na cewa “Mun fahimci a yau, za a samu ‘ya’ya maza da mata wadanda ba za su iya ziyartar iyayensu ba, da kuma dattawan da aka kebe daga matasa. Akwai kuma wadanda ke rayuwa hannu baka hannu kwarya kuma suna fuskantar wahala,”

“Dole ne mu sake kira kan ci gaba da mutunta umurnin takaita zirga-zirga a jihohin da wannan umurni ke aiki tare da bin shawarwarin likitoci da masana kimiyya: zama a gida da wanke hannaye da kuma kare rayukan jama’a,”

A cewarsa “‘yancin walwalarku da muke neman a yau ku takaita zai zama na wani dogon lokaci ne kawai idan masu ba da shawara kan kimiyya suka ce hakan ya zama dole. Amma suna da muhimmanci – a fadin duniya – a kawo karshe tare da yaki da yaduwar cutar,”

Shugaban ya kara da cewa gwamnati ta yi wa dimbin marasa karfi da ke yankunan da matakin kullen ya shafa tanadin tan 70,000 na hatsi wanda za a rarraba ga wadanda suke da tsananin bukata da kuma rarraba kudaden tallafi da gwamnatin tarayya ke yi a jihohin da kananan hukumomi.

“Muna rokonku ku saurari sanarwar da ake a kafafen yada labarai kan hanyoyin samun tallafin gwamnatin da kuma sanin irin tallafin da gwamnati ta tsara yi a nan gaba,”.

“Juriyar da gwamnati take so daga gare ku saboda a fadin duniya babu wata hanya daya tilo ta yaki da annobar. Babu rigakafi kuma hakan na nufin akwai zabi da za a yi: tsakanin ci gaba da tafiyar da lamura kamar yadda aka saba ko rungumar takunkumin da aka sanya na takaita zirga-zirga duk da hana ya yi mummunan tasiri da ba a yi tsammani ba.” a cewar sanarwar.

“Amma a wannan lokaci na rashin dadi, ya zama dole a gare mu,  mu fada muku gaskiya ba tare da boye-boye ba: wannan annoba ce ta duniya baki daya. Ta shafi kasashe 210 da yankuna a sassan duniya. Ba za mu nade hannu muna jiran taimakon wasu ba. Mu ne kadai za mu iya yakar cutar,”

“A maimakon haka, kawar da kwayar cutar ya ta’allaka a kanmu. Ba za mu jira wasu ba. Za mu iya dogara ne da kanmu. Kuma hakan ya zama dole a yi kuma za mu yi nasara ta kawo karshen barkewar cutar a matsayinmu na ‘yan Najeriya tare.”

Ya zuwa yanzu dai mutum 318 ne suka kamu da coronavirus a kasar – mutum 70 sun warke sai wasu 10 da suka mutu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here