Isah Ahmed Daga Jos
GWAMNAN Jihar Filato Simon Lalong ya kaddamar da aikin feshin magungunan kashe kwayoyin cuta, a kasuwanni da wuraren zaman jama’a a garin Jos da kewaye, a matakan da gwamnatin jihar take dauka, na ganin cutar annobar Korona ba ta shigo jihar ba. Gwamnan ya kaddamar da wannan aiki ne, a babbar kasuwar Jos ta Taminus, a ranar Juma’ar nan.
Da yake jawabi a wajen, Gwamna Simon Lalong ya bayyana cewa a shirye gwamnatinsa take, wajen ganin ta fito da tsare-tsare na ganin annobar cutar korona, ba ta yadu a jihar ba.
Ya ce sun shirya tunkarar dukkan wani rahoton billar wannan cuta a jihar, don ganin sun dauki matakin magance ta nan take.
Ya ce duk da cewa har ya zuwa wannan lokaci, babu rahoton bullar wannan cuta a jihar Filato, amma hakan ba zai sanya su kwanta, ba tare da sun yi shirin komai ba.
‘’Don haka muka kafa dokar hana fita tare da rufe jihar nan gaba daya, domin a yi feshin magungunan kashe cututtuka a dukkan kasuwanni da hanyoyi da wuraren zaman jama’a da ke jihar nan. Don haka muna kira ga al’ummar jihar nan su zauna a gidajensu, domin ganin an sami nasarar wannan aiki’’.
Gwamna Lalong ya yi bayanin cewa nan da ‘yan kwanaki masu zuwa, za a bude cibiyar gwada wannan cuta ta korona a Filato, don gano masu dauke da wannan cuta a cikin gaggawa.