Jihohi 16 Da Babu Cutar Korona Bairos A Nijeriya

0
685

Rahoton Z A Sada

KIMANIN jihohi 16 ne cikin jihohi 36 gami da Abuja ya zuwa yanzu ba su dauke da cutar nan ta korona bairos da ta addabi duniya. Sannu a hankali cutar na ci gaba da yaduwa a jihohin Najeriya bayan fara bullarta a Legas da Ogun da suke kudancin kasar.

Annobar ta fara bulla ne ranar 27 ga watan Fabrairun 2020, kuma zuwa ranar Talata 13 ga watan Afrilu, jihohi 19 ne da kuma Abuja aka tabbatar da bullar cutar coronavirus a Najeriya mai yawan jihohi 36 hadi da Abuja babban birnin Tarayya.

Alkaluma na baya-bayan nan daga hukumar da ke dakile yaduwar cututtuka a Najeriya ta ce mutum 343 suka kamu da cutar a jihohi 19 na kasar hadi da Abuja. An sallami 91 daga cikinsu.

Zuwa ranar Talata 13 ga watan Afrilu cutar Covid 19 kashe mutum 10 a Najeriya.

Sai dai har yanzu akwai jihohi 16 na Najeriya da cutar ba ta shiga ba, wadanda suka hada da:

1. Abia

2. Adamawa

3. Bayelsa

4. Borno

5. Kuros Riba

6. Ebonyi

7. Gombe

8. Imo

9. Jigawa

10. Kebbi

11. Kogi

12. Nassarawa

13. Filato

14. Sakkwato

15. Yobe

16. Zamfara

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here