Kungiyar Fulani  Ta ‘Gan Allah’ Ta Bukaci A Bude Kasuwannin Shanu Na Najeriya

0
627
Alhaji Sale Bayari

 Isah Ahmed Daga  Jos

 

KUNGIYAR ci gaban al’ummar  Fulani makiyaya ta Najeriya ta ‘Gan Allah’, ta bukaci gwamnatocin jihohin kasar nan,  su bude  kasuwannin sayar da shanu da suka rufe, sakamakon bullar annobar cutar korona. Kungiyar ta bayyana wannan bukata ce, a cikin wata sanarwar bayan taron kasa, da ta gudanar a garin Jos babban birnin Jihar Filato, wadda ke dauke da sanya hanun shugaban kungiyar Alhaji Sale Bayari.  

Kungiyar ta ce bayyana wannan bukata ya zama wajibi, musamman  ganin irin mawuyacin halin rayuwa da al’ummar Fulani makiyaya suka shiga, sakamakon daukar wannan mataki na rufe kasuwannin sayar da shanu a kasar nan.

‘’Abin da mamaki gwamnati ta rufe kasuwannin sayar da shanu, amma ta bar wuraren sayar da kayayyakin abinci a bude. Ya kamata gwamnati ta gane muhimmancin naman da shanu suke samarwa a wajen hada abincin da al’ummar kasar nan suke ci’’.

Kungiyar ta yi bayanin cewa ta lura al’ummar Fulani makiyaya ba sa cikin tsarin shirye-shiryen tallafa wa al’ummar kasar nan, da gwamnatin tarayya take gudanarwa. Don haka ta bukaci ayi gyara kan wannan al’amari, Kuma a yi gaggawar sake bude wadannan kasuwannin shanu da aka rufe. 

Daga nan kungiyar ta yi kira ga al’ummar Fulani makiyaya, su rika yin aiki da dukkan shawarwari da matakan da gwamnati ta dauka na magance yaduwar wannan annoba, ta cutar korona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here