Wautar Wasu Tsiraru Na Iya Janyo Halakar Jama’a – Buhari

0
606

Rahoton Z A Sada

SHUGABA Buhari ya ce zuwa yanzu sun gano kashi 92% na mutanen da suka yi hulda da masu fama da korona, tare da ninka yawan dakunan gwaje-gwaje a Najeriya.

Ya kuma bayyana fatan kara yawan gwajin masu cutar korona zuwa mutum 1,500 kullum a fadin kasar.

Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne yayin jawabin da ya gabatar da marecen ranar Litinin inda ya sanar da tsawaita matakin kulle jihohin Legas da Ogun da kuma Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Shugaban ya ce sun horas da ma’aikatan lafiya sama da 7,000 kan rigakafi da matakan dakile cutuka masu yaduwa, yayin da hukumar NCDC ta aika jami’anta zuwa jiha 19 a kasar.

Jawabin na zuwa ne daidia lokacin masu cutar korona suka karu zuwa sama da mutum 340 a fadin Najeriya.

coronavirusHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

A cewarsa: “Legas da Abuja a yau suna da karfin karbar marasa lafiya dubu guda a fadin cibiyoyin kwantar da masu cutar korona da ke fadin biranen biyu”.

Ya kuma ce ta hanyar amfani da dukiyar kasar da kuma gudunmawar da suka samu, za su wadata cibiyoyin ciki har da na jihohi da ma’aikata da kayan aiki a ‘yan makwanni masu zuwa.

Buhari ya ce tuni suka samar wa ma’aikatan lafiya a dukkanin cibiyoyin kula da masu korona rigunan kare lafiya don su sanya, su gudanar da ayyukansu cikin aminci.

“Fata da addu’o’inmu su ne ba sai mun yi amfani da wadannan cibiyoyi ba, amma dai duk da haka za mu shirya don gudun abin da ka je ya zo” in ji shi.

Ya ce a matsayinsu na zababbun shugabanni sun tsaida wannan shawara ce mai wahalar gaske duk da yake sun sani za ta hargitsa harkokin rayuwa kuma ta sanya ‘yan kasa da ababen kaunarsu da al’ummominsu cikin takura.

@MBuhariHakkin mallakar hoto@MBUHARI

Sai dai a cewar shugaban wannan sadaukarwa ce ake bukata don takaita bazuwar cutar kobid-19 a kasar. “Sun zama dole don kubutar da rayuka”.

Buhari ya ce: “manufarmu har yanzu ita ce shawo kan bazuwar korona da kuma samar da sarari, lokaci da kayan aiki don daukar gagarumin mataki na bai daya.

Ya ce sakamakon gagarumin goyon baya da hadin kan da suka samu, sun cim ma dumbin nasarori a cikin kwana 14 da aka kulle biranen tun da farko.

A cewarsa, kasar ta hau kan hanya don samun nasara a yaki da annobar.

Sai dai ya ce duk da haka har yanzu yana cike damuwa kan karuwar mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar da kuma wadanda suka rasu a fadin duniya da ma musamman a Najeriya.

Yadda babbar hanyar Ikorodu ta Legas ta zama wayam sakamakon dokar hana fita da aka saka a jihar.Hakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Yadda babbar hanyar Ikorodu ta Legas ta zama wayam sakamakon dokar hana fita da aka saka a jihar.

“A ranar 30 ga watan Maris 2020, lokacin da muka daukar matakin kullewar kamar yadda likitoci da masana kimiyya suka ba da shawara, jimillar masu cutar a fadin duniya sun dan haura 780,000.

To amma jiya, adadin masu cutar a fadin duniya ya zarce 1,850,000. Wannan adadi ya fi karfin ninki biyu.”

Ya ce a cikin kwana 14 kawai, fiye da mutum 70,000 cutar korona ta yi ajali. Kuma a dai wannan lokaci, mun ga yadda kwayar cutar sha kan harkokin kula da lafiya hatta a kasashe mafi karfin arziki.

Muhammadu Buhari ya ce a Najeriya, akwai mutanen da suka kamu da cutar korona 131 a jiha 12 ranar 30 ga watan Maris, mutum biyu kuma sun riga mu gidan gaskiya.

“Da safiyar nan Najeriya tana da mutum 323 da ke da cutar a cikin jiha 20. Abin takaici kuma a yanzu muna da mutum da suka rasu,” in ji shugaban.

Ya ce jihar Legas na da kashi 54% na mutanen da aka tabbatar sun kamu da korona a Najeriya. Idan aka hada da na Abuja, wuraren biyu na da sama da kashi 71% na wadanda suka kamu.

Don haka: “Mafi yawan kokarinmu zai fi karkata zuwa wadannan wurare guda biyu”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here