‘Yan Sanda Sun Gano Sunayen Manyan ‘Yan Siyasa A Gidan Matsafa

0
599

Mustapha Imrana Abdullahi Da Z A Sada

RUNDUNAR ‘yan sanda ta kasa a Jihar Zamfara karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sanda Usman Nagoggo sun bayyana bankado sunayen wadansu manyan ‘yan siyasa a gidan matsafa.

Kwamishina Usman Nagoggo ya bayyana cewa, sun samu nasarar bankado wannan gidan ne sakamakon bayanan sirrin da rundunar ta samu.

An dai gano sunayen manyan ‘yan siyasa ne a rubuce, kuma bayanai sun bayyana cewa a duk lokacin da matsafan ke gudanar da lamarin masu za a ga kwari irin su Kadangaru da ire-irinsu na mutuwa. Haka an sami wata kwarya shake da jini da wasu layu da guraye tare da wata kwaryar mai dauke da allurai duka na tsafi.Sai dai har ya zuwa ba da wannan rahoto, ‘yan sandan da suka kai samame gidan na tsafi ba su tarar da ko da mutum daya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here