An Sallami Wanda Cutar Korona Ta Kama A Kaduna

0
426
Mustapha Imrana Abdullahi
GWAMNAN Jihar Kaduna ta bayyana cewa an sallami wani mutum daya daga cikin mutane shida da cutar Korona ta kama, an dai sallame shi ne daga wurin da aka killace wadanda suka harbu da Covid – 19.
Kwamishinar lafiya Dakta Amina Mohammed Baloni ta bayyana hakan ranar Laraba, ta ce an samu nasara ne sakamakon irin kulawar da ya samu a wurin da aka killace masu fama da cutar.
Kamar yadda ta bayyana cewa ” an samu nasara ne bayan irin gwajin da aka yi masa had sau biyu kuma sakamakon ya nuna hakan, sakamakon dai ya zo ne a jiya Talata ranar 14 ha watan Afrilu, 2020.
” Muna kokarin ganin suma sauran an ci gaba da yi masu aikin kulawar kamar yadda ya dace dukkansu idan sun samu sauki sai a yi masu Gwaje gwajen da ya dace a sallame su”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here