An Sassauta Dokar Hana Fita A  Kaduna Na Kwana 2 Don A Siya Kayan Abinci

0
418

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GWAMNATIN jahar Kaduna ta sassauta dokar hana walwala da ta sanya a fadin jahar, sakamakon annobar COVID-19.

Hakan zai kama daga ranar Talata, 14 ga watan Afrilu, zuwa ranar Laraba, 15 ga watan Afrilu, Channels TV ta ruwaito.

Kwamishinan harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Talata, ya bayyana cewa an sassauta dokar hana zirga-zirgan na kwanaki biyu ne.

Domin mutane su samu damar siyan kayayyakin abincin da za su ajiye a gidajensu da sauran kayayyakin amfani kafin a ci gaba da dokar hana fitan a ranar Alhamis.

Ya kara da cewar shagunan siyar da abinci da magunguna ne kadai aka ba izinin bude shagunansu daga karfe 8:00 na safe zuwa 6:00 na yamma a wadannan ranaku.

A cewarsa, hakan na daga cikin manufar da aka amince da shi na sassauta dokar hana fita na kwanaki biyu a kowani mako, domin ba al’umma damar siyan abubuwan amfani da suka kare.

Gwamnatin jahar ta kuma shawarci mazauna jahar da su nisanci taron jama’a a yayinda suka je siyayya, sannan kuma cewa motocin haya su bi dokar mutum biyu a kowani layin mota.

A yayinda suke martani ga umurnin gwamnati, mazauna garin Kaduna sun yi korafin cewa suna wahala saboda rashin kudin siyan kayan abinci.

Sun bukaci gwamnatin da ta tallafa masu da karin kayan tallafi zuwa lokacin da za a cire takunkumin baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here