Annobar Kurona: Kungiyar Ci Gaban Yankin Funtuwa Ta Tallafa wa Magidanta 100

0
530
Imam Ibrahim Awwal [Usama]

Isah Ahmed Daga Jos

KUNGIYAR ci gaban yankin Funtuwa da ke Jihar Katsina, ta shiyar babban birnin tarayya Abuja ta tallafa wa magidanta 100 na yankin, da kudi naira dubu 15 kowannen su, don saukaka masu  mawuyacin halin da aka shiga  na zaman gida, sakamakon guje wa yaduwar cutar korona. Shugaban Kungiyar, Imam  Ibrahim Awwal [Usama] ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce sun kirkiri wannan kungiya  ce don taimakon al’umma, bisa lura da wannan yanayi da Allah ya kawo,  wanda duniya ta rude, sakamakon annobar Kurona, inda  gwamnatocin tarayya da jihohi  suka ba da umurnnin, kowa ya zauna a gida.

Ya ce don haka kungiyar ta  lura   cewa akwai mutane da dama a Nijeriya, wadanda sai sun fita su iya ciyar da iyalansu, don haka ta basu wannan tallafi.

 Ya ce a karqashin wannan tallafi da suka bayar  an baiwa kowanne daga cikin  iyayen kungiyar  Naira 20,000 domin su  sayi abincin da zasu ciyar da iyalansu.  A ya yinda sauran  ‘yan kungiyar aka bai wa  kowane  Naira 15,000 wadanda  sun kai  mutum 100. Kuma an aiwatar da wannan shiri ne, ta hanyar tura masu kudaden  ta asusun ajiyarsu  ta banki.

‘’Muna  kira ga  ‘yan kungiyar kan  bin matakan kariya da riga-kafin kamuwa da wannan cuta, ta Kurona. Wannan kungiyar ta tanadi likitoci na musamman da zasu rika duba ‘yan wannan kungiya, idan bukatar hakan ta taso. Duk  wanda yake karkashin wannan kungiya, idan ya ji wani yanayi a jikinsa da bai gane ba,  za a bayar da lambobin ‘yan kungiyar da za a  kira, zo su duba mai kiran’’.

Imam   Usama ya yabawa ‘ya’yan kungiyar kan goyan baya da hadin kan  da suke bayarwa, wajen samun nasarar ayyukan kungiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here