COVID-19: Ya Zuwa Yau Babu Mai Dauke Da Cutar A Jihar Yobe..inji Gubana

0
302

Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu

MATAIMAKIN Gwamnan jihar Yobe, kuma shugaban kwamitin dakile yaduwar cutar nan ta Covid-19 a Jihar Hon. Idi Barde Gubana ya bayyana cewa
har ya zuwa yau babu wani mai dauke da wannan cutar a fadin jihar.
Shugaban kwamitin na yaki da cutar ta Covid-19 ya kuma yabawa al’ummar Jihar bisa cikakken hadin kai da goyon baya da suke bai wa kwamitin, dangane da matakan  da  ya  ke  dauka  don dakile  yaduwar  korona  a  jihar.
Mataimakin gwamnan ya bayyana hakan ne jim kadan, bayan ya gana da mambobin kwamitin, a babban dakin taro dake gidan gwamnatin jihar a
garin Damaturu.
Ya ci gaba da bayyana cewa kwamitin su ya na iya kokari tare da yin addu’o’i, babu dare babu rana  wajen  ganin  cewa wannan cutar ba ta shigo jihar ba tare da addu’o’in al’ummomin Jihar.
Ya kara da cewa, duk da hakan, wani babban abin takaici wasu batagari su na yada  jita-  jita a kan annobar, Haka kuma, shugaban kwamitin  ya  yikira  ga  jama’ar jihar Yobe, da cewa su guji yada jita -jita,
karya ko kazafi, wanda ya ce hakan ya na jawo barazana da fargaba a zukatan al’umma, sannan hakan ya saba da koyarwar addini da al’adar
zamantakewa tsakanin al’umma.
Shugaban kwamitin yaki da cutar ta Covid-19 ya kara da cewa yaki da wannan hattsabibiyar  cutar  hakki  ne matuka wanda ya rataya akan kowane dan Nijeriya, ta hanyar bada shawarwari, wayar  da  kan jama’a da  kuma  bin hanyoyin da masana kiwon lafiya su sanar don kariya da makamantansu.
A nasa bangaren kuma, mataimakin shugaban kwamitin kuma kwamishina a ma’aikatar kiwon lafiya a jihar Yobe, Dr. Mohammed Lawan  Gana  ya  yi  wa ‘yan jaridu  karin  bayani  dangane da halin da ake ciki yanzu da cewa, ‘’ a halin da ake ciki yanzu haka, babu ko mutum guda da ya ke dauke da cutar
korona a fadin jihar Yobe. Saboda ita wannan cuta ce wadda sai ta hanyar gwaji ake ganota, kuma za ka tarar akwai kamanceceniyar alamun cutuka
daban-daban, ba sai Cobid-19 ba kadai’’.
Mataimakin shugaban kwamitin ya kara  da  cewa,  bisa  ga hakan, ya na da kyau jama’a su guji yada maganganun da ba su da tushe balle makama, kuma wannan kwamiti nasu zai ci  gaba  da  bada  sahihan bayanan da su ka shafi matsalar, a kafofin sadarwa daban-daban don fadakar da jama’ar jihar Yobe kwata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here