Gobara Ta Lashe Gidaje 700 A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira A Borno

0
328
Daga Usman Nasidi.
AKALLA gidaje 700 ne suka lalace a yayin da gobarar da ta tashi a sansanin ‘yan gudun hijira da ke karamar hukumar Mafa na jihar Borno.
Sakataren gundunmar, Mohammed Lawan Sharrif ne ya bayyana hakan yayin hirar da ya yi da manema Labarai, a ranar Talata a Maiduguri.
Mista Lawan Sheriff ya ce gobarar da ta fara ci tun karfe 11 na safiyar ranar Talata ta kuma dauki awanni tana ci ta kone gidaje da dama a sansanin.
Ya ce gobarar da ta fara daga gida guda daya ta yadu zuwa sauran gidajen saboda babu jami’an hukumar kashe gobara a lokacin da lamarin ya faru.
Ya ce sauran mazauna sansanin gudun hijirar, jami’an sa kai na Civilian JTF, jamian tsaro da sauran alumma ne suka taimaka aka kashe gobarar.
Ya ce, “Muna jin cewa gobarar ta tashi, mun tattara mutane daga unguwar da sansanin ya ke domin zuwa wurin da gobarar ta tashi domin a kashe ta. Kawo yanzu babu wanda ya mutu.”
Sakataren ya ce ofishinsa da sauran abokan hulda suna aiki tare domin ganin sun tallafa wa wadanda abin ya shafa da kayan masarufi da wasu abin da za su bukata na yau da kulum.
Ya ce, “Mun umurci manajojin sansanin guda 11 su yi nazarin abinda aka yi asara kuma su kirga mutanen da ke sansanin domin tabbatar da cewa kowa yana nan lafiya kuma an kawo motar daukan marasa lafiya.”
Akwai mutane 4,782 a sansanin gudun hijirar  Mafa galibinsu mata ne da yara da kuma tsofaffi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here