Gwamnatin Tarayya Ba Za Ta Iya Raba Wa ‘Yan Najeriya Kudaden Tallafi Da Aka Tara Ba

0
319
Daga Usman Nasidi.
MINISTAN labarai, Lai Mohammed, ya ce gwamnatin tarayya ba za ta iya raba wa ‘yan Najeriya kudaden tallafi da hukumomi masu zaman kansu suka bayar don yakar cutar korona bairos ba.
A cewar, ministan ya bayar da dalilan da ya sa ba za a ba al’umman kasar kudin ba, a lokacin da ya bayyana a shirin “Politics Nationwide”, na ‘Radio Nigeria’ a ranar Talata.
Ya yi martani ne ga wata bukata da ke neman a raba wa ‘yan Najeriya wani bangare na kudaden domin su toshe gibin da dokar hana fita ya yi masu.
Ministan ya ce kudaden na inganta harkar lafiya ne, sannan cewa ba za a iya amfani da su wajen samar da kayan rage radadi ba.
Mohammed ya ce tawagar shugaban kasa kan coronavirus ba su da iko a kan kudin , kuma cewa ba za su iya raba wa kowa ko sisi daga kudin ba.
Ya ce a kokarin rage wa mutane radadi, kowace kasa na da tsarin da ta amince da shi wajen yin hakan.
Ya ce gwamnatin tarayya ta dauki matakai da dama domin rage wa mutane radadin COVID-19, wanda suka hada da raba kayan abinci, kudade da kuma dauke wa mutane biyan bashi.
Ya ce Najeriya ce kan gaba a Afrika ta bangaren rage wa al’ummarta radadi yayin da duniya ke yaki da annobar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here