Karamar Hukumar Jos Ta Fara Raba Wa Al’umma Ruwan Sha

0
386
Alhaji Shehu Bala Usman

Isah  Ahmed Daga Jos

GANIN matsanancin karancin ruwan sha da ake fama da  a garin Jos babban birini Jihar Filato, sakamakon dokar hana fita, da aka sanya a jihar Filato. Karamar Hukumar Jos ta Arewa ta dauki nauyin raba wa al’ummar karamar hukumar, ruwan sha. Shugaban karamar hukumar Alhaji Shehu Bala Usman ne, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa, da wakilinmu.

Ya ce tun a ranar Lahadi suka fara raba wannan ruwan sha a  unguwannin da ke cikin garin Jos, da ba su da ruwan famfo.

 Ya ce unguwannan da suke raba wannan ruwa sun hada da Unguwar Rogo da Ali Kazaure da Tudun Wada da Kabong da Jenta Adamu da Zinariya da Randar Ruwa.

Ya ce suna samun wannan ruwa ne a hukumar ruwa ta Jihar Filato, inda suke biya a dauko ana  rabawa a wadannan unguwanni, don saukakawa jama’a.

Ya ce ba  maganar ruwa kadai ba, karamar hukumar,  tun lokacin da aka kafa wannan doka, tayi wani abu na tallafawa jama’a, mabukata da kayan abinci, domin a  saukaka wa  jama’a.

‘’Mu kanmu   wannan abu na hana fita,  baya yi mana dadi, ya zama dole ne. Don haka muna bai wa jama’a hakuri. Gara jama’a su yi hakuri, da a zo a sami wannan matsala. Domin idan aka sami wannan matsala, hankalin jama’a sai ya fi tashi fiye da wanda ake ciki yanzu’’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here