Ramadan: Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Musulmi Su Ci Gaba Da Bin Dokokin Kare Kai Daga Cutar Korona

0
312
Daga Usman Nasidi.
GWAMNATIN tarayya ta gargadi Musulmai a kasar da su guji taron jama’a da kuma tarukan addini a matakin hana yaduwar cutar coronavirus, cewa sai suna raye ne za su ga watan Ramadana.
Shugaban kwamitin fadar shugaban kasa a kan COVID-19, Dakta Sani Aliyu, ya bayyana hakan a Abuja a ranar Litinin, 13 ga watan Afrilu, a wajen taron kwamitin na 10.
Aliyu ya bukaci Musulmai a fadin kasar da su ci gaba da bin dokar hana zirga-zirga da sauran matakan da gwamnati ta gindaya a lokacin Ramadana.
A cewarsa, nisantan mutane na da matukar muhimmanci, sannan kuma cewa akwai bukatar ci gaba da hakan a wannan lokacin.
Kan azumin watan Ramadana mai zuwa da kuma tsoron Musulmai a yanzu da aka tsawaita dokar hana fita a Abuja, Lagas da Ogun, Aliyu ya ce ya zama dole a kare mutane.
Ya jadadda cewa sai mutum na raye ne zai ga Ramadanan wannan shekarar da wasu masu zuwa a gaba.

Hakkin Mallakar Hoto: Kwamared Usman Nasidi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here