Uwargidan El-Rufa’i, Ta Caccaki ‘Danta Da Ya Yi Barazanar Fyade

0
302
Usman Nasidi, Daga Kaduna.
UWARGIDAN gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Isma El-Rufai ta yi martani mai zafi ga danta a kan barazanar da ya yi wa wani a tuwita.
Matar gwamnan, wacce da farko aka fara caccaka a kan kare danta da ta yi a ranar Lahadi, ta ba da hakurin cewa sai daga baya ta karanta wallafar danta da kyau.
Daga nan ne ta zauna tare da tattaunawa da shi, sannan ta fahimci abin da ke faruwa.
Ta ce ba za ta goyi bayan cin zarafi ba kowanne iri kuwa.
A yayin da muhawarar siyasa ta fara ne Bello El-Rufai ya bayyana gazawar shugaban kasar Amurka a yakar annobar Coronavirus.
Lamarin ya koma fada tsakaninsa da wani ma’abocin amfani da tuwita din.
Abokin fadan ya ce Trump ya fi shugaban kasa Muhammadu Buhari kokari da kuma mahaifin Bello, Gwamna Nasir El-Rufai.
Bello ya mayar da martani inda yake cewa: “Ka sanar da mahaifiyarka zan mika ta ga abokaina da daren nan”.
Masu amfani da kafar sada zumuntar sun fara jawo hankalin matar Gwamnan ga wallafar da danta ya yi.
Ta ce: “Duk masu magana a kan Bello El-Rufai, su daina ambatona. Abin da ka shuka, shi za ka girbe. Komai daidai ne a soyayya da yaki. Ka mutunta kowa amma kada ka amince a taka ka. Ban ga wata barazanar fyade ba.”
Amma daga bisani sai uwargidan Gwamnan ta wallafa: “A lokacin da na yi wannan rubutun, a zatona fadan da aka saba yi ne a twitter. Na tattauna da Bello. Kada ya sake amfani da barazanar fyade a matsayin makamin yaki”
Ta kara da cewa, “Na ga yadda wallafata ta yadu kuma ina ba da hakuri ga wadanda ransu ya baci. Ina kara jaddada cewa, ba zan goyi bayan cin zarafi ba kowanne iri kuwa”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here