Wani Kansila Ya Yi Wuf Da Kayan Abincin Da Aka Ba Shi Ya Raba Wa Mutane A Jihar Neja

0
430

Daga Usman Nasidi.

WANI Kansila a karamar hukumar Katcha ta jihar Neja ya bace bat da kayan abinci da aka ba shi ya raba wa mutanen yankinsa domin saukake radadin dokar zama a gida da gwamnati ta sanya.
Gwamnatin jihar ta sanya dokar ta baci ne domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a jihar.
Kansilan na cikin kwamitin da aka nada domin rabawa mutane kayan masarufi a yankin.
Sakataren gwamnatin jihar wanda shi ne shugaba kwamitin yakin COVID-19 a jihar, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya tabbatar da aukuwan haka kuma ya ce wannan abin takaici ne.
Alhaji Ahmed Ibrahim ya nuna bacin ransa kan abin da Kansilan yayi inda y ace yanzu al’ummarsa zasu sha wahala saboda halin ha’inci da rashin godiyan Allah na shugabansu.
A cewar, an bai wa kowani yankin mazabu 274 dake kananan hukumomi 25 na jihar buhun Shinkafa 10, Masara 10, da Gero 10 kuma an nada kwamitocin rabawa a kowace karamar hukuma.
“An nada kwamitoci a dukkan yankuna 274 dake jihar. Kwamitin ya hada da Kansila, Mhugaban jam“iyya, Maigari, da Malamin addini domin raba wa mutane kayan hatsin.“
SSG Ahmed ya ce jami’an tsaro sun bazama neman Kansilan kuma zai fuskanci fushin hukumar idan aka kama shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here