Za A Dakatar Da Tafsirin Al-Kur’ani A Masallacin Sultan Bello Kaduna

0
424
Rahoton Z A Sada Da Usman Nasidi, Daga Kaduna.
KWAMITIN Masallacin Sultan Bello da ke garin Kaduna ta yanke shawarar dakatar da gudanar da tafsirin Al-Qur’ani mai girma kamar yadda aka saba yi a cikin Masallacin.
Sheikh Ahmad Gumi ne yake gudanar da tafsiri a Masallacin a duk lokacin azumin watan Ramadana, amma an samu sauyi a azumin bana saboda COVID-19.
Babban limamin Masallacin, Farfesa Muhammad Sulaiman Adam ne ya bayyana haka, inda ya ce a bana Malam Ahmad Gumi zai gudanar da tafsirin ne daga wani wuri na daban.
Sulaiman ya ce Malam Gumi ne kadai zai gudanar da Tafsirin tare da majabakinsa, kuma za a watsa karatun a kafafen sadarwa na gani da na saurare, da shafukan sadarwar zamani.
Hakazalika, Sheikh Sulaiman ya kara da cewa Masallacin Sultan Bello zai ci gaba da zama a garkame har sai lokacin da gwamnati ta bayar da izinin bude Masallatai.

Daga karshe Shehin Malamin ya bayyana dalilin daukan wannan mataki shi ne don dakile yaduwar cutar, don haka ya nemi Musulmai su ci gaba da addu’a domin Allah Ya yaye masifar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here