A Killace Duk Bakon Da Ya Shigo Karamar Hukumar Lere-Daraktan Lafiya

0
858
Alhaji Abdullahi Sani

Isah Ahmed Daga Jos

DARAKTAN kiwon lafiya na Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna kuma Sakataren kwamitin ko ta kwana na  hana yaduwar cutar annobar korona, a karamar hukumar Alhaji Abdullahi Sani, ya bayyana cewa sun bai wa sarakuna da dagatai da masu unguwanni, shawarar cewa duk bakon da aka ga ya shigo karamar hukumar  daga wani waje, musamman daga wuraren da cutar annobar korona ta bulla a killace shi, har sai ya yi makonni biyu, kafin a bari ya shiga jama’a, don guje wa yaduwar wannan cuta. Alhaji Abdullahi Sani ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce kwamitinsu  yana  ilmantar da  jama’ar gari  kan duk wani baqo da ya shigo a riqa kiwonsa domin aji daga ina ya fito? Idan ya fito daga wuraren da wannan ciwo ya bulla ne? Sarki da Mai unguwa su sanya a killace shi, na tsawon mako biyu, kafin ya yi hulda da jama’a.

Ya ce duk da har ya zuwa wannan lokaci, Allah ya kiyaye babu labarin bullar wannan cuta a qaramar hukumar. Amma sun tura ma’aikatan kiwon lafiya, zuwa kan iyakokin jihohin Filato da Bauchi da Kano da suke shigowa wannan karamar hukuma. Suna gwada dukkan mutanen da suke shigowa, don ganin ba a bari wani mai dauke da wannan cuta, ya shigo ba.

‘’Wannan kwamiti wanda mai girma gwamnan Jihar Kaduna, ya ba da umurnin a kafa, karkashin jagorancin  shugaban karamar hukumar Lere, wanda ke kun she da jami’an kiwon lafiya da  wakilin manyan sarakuna da shugabannin addini da jami’an tsaro, yana nan yana aiki ba dare ba rana, wajen ganin wannan cuta bata shigo ta yaxu, a wannan karamar hukuma ba’’.

Ya yi kira ga al’ummar qaramar hukumar, su ci gaba da basu goyan baya da hadin kai, kan wannan aiki da suka sanya a gaba, kuma  su daina taruwa ana cunkoso a wurare. kuma duk wanda aka ga yana da alamun  ciwon a sanar da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here