Gwamnatin Filato Ta Daga Dokar Hana Fita Zuwa Ranar Lahadi

0
369

Isah Ahmed Daga Jos

GWAMNATIN Jihar Filato ta daga  dokar hana fita a jihar,  daga ranar Alhamis din nan zuwa ranar Lahadi mai zuwa. Gwamnan Jihar Simon Lalong ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga al’ummar jihar,  a gidajen rediyo da talbijin  kan cikar wa’adin dokar hana fita na mako daya da ya sanya a jihar, a yammacin ranar Larabar nan.

Ya ce gwamnatin ta daga dokar ne domin ta bai wa jama’ar jihar, dama su fita su sarara, su sami damar sayen kayayyakin abinci.  Daga daren ranar Lahadin kuma dokar ta ci gaba da aiki, har ya zuwa ranar 23 ga watan Afrilu, kamar yadda jami’an kiwon lafiya, suka bayar da shawara.

 A makon da ya gabata ne dai gwamnatin ta jihar Filato, ta kafa dokar hana fita na wa’adin tsawon mako daya.  A matakan da take dauka na ganin cutar annobar Kurona, bata shigo jihar ta yadu ba.

Gwamnan ya ce a lokacin da aka gudanar da dokar, an sami damar killace jihar gabaki daya tare da kula da wadanda ake tsammanin suna dauke da wannan cuta da kuma yin feshen magungunan kashe cututtuka a kasuwanni da wuraren zaman jama’a.

‘’Mun binciki mutane 99 kan wannan annoba a lokacin wannan kulle, inda muka killace mutane 23, da suka shigo jihar nan, daga jihohin da wannan annoba ta bulla. Har ya zuwa wannan lokaci babu wani alamun wannan cuta tattare da wadannan mutane. Muna godiya ga Allah da ya sa har yanzu, babu rahoton bullar wannan cuta a wannan jiha.

Gwamna Lalong ya nuna matukar farin cikinsa ga al’ummar jihar, kan irin goyan baya da hadin kan da suka bayar, a lokacin da aka sanya wannan doka ta hana fita.

Gwamnan ya nuna takaicinsa kan yadda aka hukumta mutane 837, da suka karya wannan doka ta hana fita.

 Ya ce gwamnatin  ba za ta taba saurara wa dukkan wanda, ya karya wannan doka ba, wajen yin hukunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here