Matashin Manomi Ya yi Kira Da A Fadada Dam Din Kunnawa.

0
458
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
WANI matashin manom Malam Abdullahi Muhammad Inuwa Kunnawa Majema ya bukaci gwamnatin tarayya da ta jihar Kano da kuma karamar hukumar Dawakin Tofa dasu hada hannu domin kara fadada dam din Kunnawa dake yankin karamar hukumar Dawakin Tofa domin bunkasa Norman rani da kiwon dabbobi.
Matashin manomin kuma dan siyasa ya yi wannan kira yayin da ya kai ziyara Dam din na Kunnawa  domin ganin halin da yake ciki  tun bayan  gyaran da gwamnatin tarayya ta  yiwa gurin kuma  daga bisani  ya kafe saboda noman rani da aka yi a wajen wanda hakan ta sanya manoma masu tarin yawa suka yi asara mai tarin yawa na abin da suka noma saboda rashin ruwa.
Bugu da kari, matashin wanda kuma yake da kishin al’umar wannan yanki, ya bayyana cewa idan har aka hada hannu aka fadada wannan dam na Kunnawa ko shakka babu manoma da makiyaya dake yankin zasu kara bunkasa noman su duk shekara sannan za’a rage yawan kwarara cikin birane neman  aikin yi, inda kuma ya jaddada cewa zai ci gaba da kokari wajen yin kiraye-kiraye ga gwamnatoci domin ganin an kara inganta gurin.
Daga karshe,Malam Abdullahi Inuwa ya yi fatan cewa kafin faduwar damina, wannan dam na Kunnawa zai sami kulawa ta musamman ta yadda manoma da makiyaya za su ci gaba da gudanar da sana’o in su na noma da kiwo don wadata kasa da abinci da bunkasa tattalin arziki da kuma samar da aiyukan yi ga dimbin al’uma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here