Rahoton Z A Sada
MALAMAN addinin Musulunci da dama a Najeriya masu gabatar da tafsirin Alkur’ani mai girma a watan Ramadana kowace shekara sun bayyana cewa ba za su tara jama’a a lokutan tafsirin da a al’adance ake gudanarwa a watan Ramalana ba.
Malaman sun ce sun dauki matakin ne domin yin biyayya ga dokar gwamnati ta hana tarukan jama’a domin dakile yaduwar cutar korona.
Gwamnati ta umarni ‘yan Najeriya su dauki matakan daban-daban wajen kauce wa kamuwa da cutar korona, ciki har da kaurace wa shiga tarukan jama’a.
Sheikh Dahiru Bauchi

A wani taron manema labarai da ya gudanar ranar Laraba, Shieikh Dahiru Bauchi ya ce “Ba za mu gudanar da tafsirin da muke yi a Kaduna ba inda daruruwan mutane suke halarta kowacce rana.”
Ya kara da cewa zai rika gudanar da Tafsirin ne a gidansa da ke Bauchi inda za a rika watsawa ta rediyo da talbijin da kuma shafukan sada zumunta.
Ko a watan Maris, Shugaban Darikar Tijjaniyyar ta Najeriya, ya sanar da jinkirta taron Maulidin Sheikh Nyass wanda da za a yi a Abuja da Sokoto saboda hana yaduwar cutar korona.
Sheikh Ahmad Gumi

A wani sakon bidiyo da ya fitar, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce a wannnan shekarar ba zai gudanar da tafsirin azumin watan Ramalana “a Masallacin Sultan Bello kamar yadda aka saba ba,” yana mai cewa za a gudanar da shi a wurin da ya dace da tsarin kiwon lafiya.
Malamin ya ce ya dauki matakin ne domin kare lafiyar kansa da ta mutanen da za su halarci wurin tafsirin, kamar yadda hukumomin lafiya suka bukaci a yi domin dakile yaduwar cutar korona.
Sheikh Tijjani Bala Kalarawi

Malamin, wanda yake gudanar da tafisiri duk shekara a birnin Kano da ke arewacin kasar, ya shaida wa BBC cewa bana ba zai tara jama’a a wajen tafsirin ba.
Ya ce zai rika gudanar da shi ne a sutudiyon da ke gidansa inda za a nada sannan a watsa ta gidajen talbijin da rediyo da shafukan intanet.
Sheikh Kalarawi ya yi kira ga sauran malaman da za su gudanar da tafsiri su yi koyi da irin su da suka yanke shawarar dakatar da tara jama’a kamar yadda gwamati ta bukaci a yi.