Cutar Korona Bairos: Allah Ya Yi Wa Shugaban Ma’aikata Abba Kyari Rasuwa

0
545
Marigayi Abba Kyari,. Ko wane ne zai kwafe ggurbinsa?
Daga Usman Nasidi Da Z A sada

SHUGABAN ma’aikatan fadar shugaban Najeriya Malam Abba Kyari ya rasu bayan ya sha fama da jinya sakamakon kamuwa da cutar korona.

Mai magana da yawun Shugaba Buhari Femi Adesina ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a da daddare da misalin 12.50 na tsakar daren, a shafinsa na Tuwita.

Abba Kyari ya rasu ne a Legas inda ya koma can bayan kamuwarsa da cutar korona ya ci gaba da jinya.

Dama rahotanni sun ce Abba Kyari yana fama da wata rashin lafiya kafin ya kamu da cutar korona, kuma masana harkar lafiya sun ce masu fama da wata cutar na daga cikin wadanda suka fi fuskantar hadarin mutuwa daga cutar ta korona.

Sanarwar fadar shugaan kasar ta ce za a sanar da lokacin jana’izarsa nan gaba kadan.

A ranar 24 ga watan Maris ne aka tabbatar da cewa shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriyar ya kamu da cutar korona bayan komowarsa kasar daga Jamus. Labarin ya ja hankalin ‘yan kasar sosai saboda girman mukaminsa.

Abba Kyari shi ne babban jami’in gwamnatin kasar na farko da ya harbu da covid-19.

Wane ne Abba Kyari?
Abba Kyari ya kasance mutum mai karfin fada a ji a gwamnatin Shugaba Buhari. Dan asali jihar Borno ne da ke arewa maso gabashin kasar. Kyari tsohon dan jarida ne, kuma tsohon ma’aikacin banki, inda ya rike manya-manyan mukamai a wasu bankunan kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here