Usman Nasidi, Daga Kaduna.
GWAMNATIN jihar Kaduna ta sanar da sallamar masu cutar Coronavirus uku dake jinya a jihar bayan an tabbatar da cewa sun samu sauki kuma sun barranta daga cutar.
Kwamishanar kiwon lafiyan jihar, Dakta Amina Mohammed-Baloni ta bayyana hakan ne a jawabin da ta saki da yammacin Juma’a, 17 ga watan Afrilu, 2020.
Jawabin yace: ” Ma’aikatar lafiyan jihar Kaduna tana mai sanar da sallamar marasa lafiya uku bayan sun warke daga COVID-19.”
“Mutane uku da aka saki na cikin mutane shida da suka kamu da cutar a jihar.”
“Gwaji biyu da aka yi musu sun nuna cewa sun tsira daga cutar kuma yanzu an sallamesu.”
“Hakan ya kawo adadin wadanda aka sallama a jihar Kaduna cikin makon nan hudu. Mutane biyu kadai suka rage kuma muna kyautata zaton nan ba da dadewa ba za’ayi.”