Al’umar Yankunan Karkara A Jihar Kano Suna Bin Dokar Zaman Gida-Bincike.

0
476
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
SAKAMAKON dokar da gwamnatin jihar Kano ta bayar na a zauna a gida na tsawon kwanaki bakwai, wakilin mu yayi wani zagaye domin duba yadda al’umar yankunan karkara suke bin wannan umarni tareda kasancewa cikin yanayi na zaman guri guda domin dakile yaduwar cutar corona virus kamar yadda abin yake a sassan duniya.
A garin Dungurawa da ke yankin karamar hukumar Dawakin Tofa kan hanyar Kano zuwa Katsina, wakilin mu ya duba yadda al’umar wannan gari suke gudanar da zaman umarni tare da tattaunawa da wasu mutane kan halin da ake ciki na zaman rayuwa tun bayan sanya dokar hana zirga-zirga tareda kaucewa shiga cunkoso kamar yadda aka umarta.
Malam Auwalu Shu’aibu, wani direban motar haya ya ce” muna zaune a gidajen mu ba tare da fita ba domin bin umarnin gwamnatin Kano na a zauna a guda tare da yin nesa-nesa da juna ta yadda za a cimma nasarar dakushe kaifin cutar Covid-19 a fadin jihar, sannan muna ta addu’ar neman kawo karshen wannan annoba daga doron kasa baki daya”. Inji shi.

Wasu Mutanen Garin Dungurawa Dake  jihar Kano, Yayin Zaman Gida Domin Bin Umarnin Gwamnatin Jihar Na Hana Zirga-zirga.

Shi ma wani matashin  dan kasuwa mai suna  Ibrahim Wadalle  ya sanar da cewa ko shakka babu mutanen karkara suna matukar bin umarnin dokar da gwamnatin jihar Kano ta kafa, sannan za su ci gaba da kasancewa masu bin dokar da aka kafa ta yadda za a cimma cikakkiyar nasarar dakile yaduwar cutar Covid-19 a cikin al’uma.
Da yake karin bayani kan lamarin, kansilan mazabar Gargari Malam Abdullahi Yahaya Dungurawa ya nunar da cewa yadda al’uma suka bi umarnin zama a gidajen su, ya tabbatar da cewa an fahimci manufofin gwamnati na dakushe yaduwar  annobar corona virus ta hanyar rage shiga cunkoso da cudanyar al’uma kamar yadda masana suke ta bayani.
Sannan ya jinjinawa gwamna Ganduje da shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa Ado Tambai Kwa bisa namijin kokarin da suke yi wajen tabbatar da cewa cutar corona virus bata yadu cikin al’uma na, tareda jaddada cewa gwamnati zata ci gaba da aikin murkushe cutar cikin yardar Ubangiji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here