COVID-19: Mataimakin Ganduje, Kwamishinoni Uku Da Diyar Ganduje Sun Killace Kansu

0
393

Daga Usman Nasidi.

MATAIMAKIN gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna, kwamishinoni uku da diyar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje sun killace kansu bayan an gano cewa sun yi mu’amala da wani mai cutar.

Mambobin kwamitin hana yaduwar cutar COVId-19 din wacce mataimakin gwamna Gawuna ke shugabanta, sun hada da Balaraba Ganduje, kwamishinan lafiya Aminu Tsanyawa, kwamishinan muhalli Kabiru Getso da Imam Wada, sakataren kwamitin.

Majiyarmu ta gano cewa sun yanke shawarar killace kansu ne bayan an gano cewa mataimakin shugaban kwamitin, Farfesa Abdulrazaq Garba Habibu na dauke da cutar.

Majiya mai karfi daga gwamnatin ta ce, “K un san tunda tare suke aiki da mataimakin shugaban kwamitin kafin ya san yana dauke da cutar, zai fi idan sauran mambobin suka kullace kansu.

“An dauka jininsu don dubawa ko suna dauke da cutar amma har yanzu ba a samu sakamakon ba.

“Muna fatan sakamakon ya nuna basu dauke da cutar. Amma ina tabbatar muku da cewa dukkan ‘yan kwamitin suna killace tare da jiran sakamako,” majiyar tace.

Idan za mu tuna, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da kwamitin a ranar 21 ga watan Maris 2020.

Alhakin takaita yaduwar annobar a jihar Kano ya hau kansu tare da duk wani kokarin zakulo masu cutar.

Kamar yadda hukumar kula tare da takaita yaduwar cutuka ta bayyana, da karfe 10:20 na daren Alhamis, an samu mutane 21 a jihar masu dauke da cutar.

A ranar Juma’a ne dokar hana zirga-zirga da gwamnan jihar Kano ta saka ta fara aiki.

An ga hotunan birnin Kano kamar an shareshi saboda jama’ar jihar sun yi biyayya ga dokar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here