Shugaban Kungiyar Manoma ta Kasa (AFAN) Ya Mika Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Abba Kyari.

0
507
Marigayi Abba Kyari,. Ko wane ne zai kwafe ggurbinsa?
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
ZABABBEN shugaban kungiyar manoma ta kasa watau All Farmers Association(AFAN), Mazayyani  Kabir Ibrahim ya mika sakon ta’aziyya ga gwamnatin tarayya da iyalai da kuma yan uwan shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya, Malam Abba Kyari, bisa rasuwar sa daren wayewar yau asabar.
A cikin sakon, shugaban kungiyar ta AFAN na kasa Mazayyani Kabir Ibrahim yayi addu’ar neman gafara ga marigayi Abba Kyari tareda fatan Ubangiji ya baiwa iyalan sa hakurin jure wannan babban rashi da kasa tayi, inda kuma ya yi kira ga daukacin al’umar Nijeriya da su ci gaba da bin shawarwarin kariya daga cutar nan mai saurin yaduwa ta corona virus ta hanyar kaucewa shiga cunkoso ko wasu gurare da ake tunanin  cewa kwai barazanar yawan al’uma.
Mazayyani Kabir Ibrahim, kuma shugaban kungiyar manoma ta kasa watau AFAN yayi jinjina ga gwamnatin tarayya da  gwamnatocin jihohin kasarnan saboda kokarin da suke yi wajen daukar matakai na dakile yaduwar cutar Covid-19 a fadin kasar nan, tareda fatan ganin an kawo karshen annobar daga doron duniya baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here