‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 1, Sun Yi Awon Gaba Da Miji Da Mata

0
313

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

WASU gungun miyagu yan bindiga sun bi cikin dare sun kai hari a unguwar Gbagyi Villa da ke cikin karamar hukumar Chikun ta jahar Kaduna, inda suka kashe mutum 1.

Hakazalika bayan bindigan sun kashe wannan bawan Allah da bai ji ba, bai gani ba, sai kuma suka yi garkuwa da wasu ma’aurata, Mata da Miji, suka tasa keyarsu zuwa cikin daji.

Lamarin ya auku ne a daren Alhamis, daidai lokacin da wasu yan miyagu suka kaddamar da hari a unguwar Dan Honu II, amma dai jama’an garin suka fatattakesu.

Shugaban kungiyar Gbagyi Villa Property owners Association, Chris Obudumu ya bayyana harin a matsayin abin takaici, sa’annan ya yi kira ga gwamnati ta kara matakan tsaro a yankin.

Obudumu yace yan bindigan sun zarce gidan wani magidanci Jack Uwenke, inda suka yi tasa keyarsa tare da matarsa, suka bar yaransu suna ta kuka.

Sai dai koda makwabtan Uwenke suka jiyo kukan yaransu, sai guda daga cikinsu, Stephen Sabastian ya yi kukan Kura ya fada ma yan bindigan, nan take suka bindige shi har lahira.

Shi ma a dan Honu, wani mutumi da yan bindigan suka kai ma hari ya bayyana cewa a lokacin da yan miyagun suka shiga gidansa sai yan sa kai da jama’an unguwa suka kawo masa dauki.

Ganin jama’a sun taru a kansu ne yasa yan bindigan suka ranta ana kare ba tare da sun gudanar da manufar da ta kai su unguwar ba.

Shugaban al’ummar Dan Honu, Akoh Salifu ya yi kira ga gwamnatin jahar Kaduna ta kara karfafa matakan tsaro a unguwar domin tabbatar da kariya ga jama’an yankin.

Idan za’a tuna makonni biyu da suka gabata yan bindigan sun yi garkuwa da wani Sufetan Yansanda, malamin kwalejin kimiyya ta Kaduna da mutane 10 a unguwar Dan Honu II.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here