Korona Bairos: An Bukaci Musulmin Duniya Su Dinga Salloli A Gida Lokacin Azumi

0
467

Rahoton Z A Sada

BABBAR majalisar koli ta malamai a Saudiyya ta bukaci al’ummar musulmin duniya a kasashen da ke fama da cutar korona su yi sallah a gidajensu lokacin watan azumin Ramadan.

Kamfanin dillacin labaran Saudiyya na SPA ya ambato majalisar manyan malaman kasar a cikin wata sanarwa na cewa ya kamata musulmi su kauracewa duk wani taron jama’a da zai kara yaduwar cutar.

Sanarwar majalisar malaman ta ce: “Ya kamata musulmi su fahimci cewa kare rayuwa babbar ibadah ce da za ta kara kusantarsu da Mahalicci.”

“Ya kamata musulmi su zama abin misali ta hanyar gudanar da addininsu yayin da suke kiyaye matakan kariya da hukumomi suka dauka a kasashen da suke,” in ji sanarwar.

Sannan majalisar ta bukaci musulmi su kauracewa duk wani taro a lokacin buda-baki ko sahur a cikin Azumi.

‘Yan kwanaki suka rage al’ummar musulmi su fara azumin Ramadan, a cikin wannan yanayi da aka killace kusan al’ummar duniya saboda annobar cutar korona inda sama da mutum miliyan biyu suka kamu da cutar a duniya.

Kusan mutum 10,000 suka kamu da cutar a Saudiyya, yayin da ta kashe mutum 97 kawo yanzu.

Tuni hukumomin Saudiyya suka hana shiga Makkah da Madina, da ma Riyadh babban birnin kasar, a kokarin da hukumomin kasar ke yi na hana yaduwar Covid-19.

Ana tababa kan yiyuwar gudanar da aikin hajji a bana, yayin da gwamnatin Saudiyya ta nemi kasashen duniya su dakatar da karbar kudaden jama’a domin zuwa aikin Hajji, a yayin da annobar cutar korona ke ci gaba da mamaye duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here