An Yi Asarar Tumatir Na Naira Dubu 900 A Kasuwar ‘Yan Tumatir Ta Jos-Nasiru Sani

  0
  654
  Alhaji Muhammad Nasiru Sani shugaban kasuwar 'yan tumatur ta farar gada Jos

  Isah Ahmed Daga Jos

  SHUGABAN Kasuwar ‘Yan tumatur ta Farar Gada, da ke garin Jos babban birnin Jihar Filato, Alhaji Muhammad Nasiru Sani ya bayyana cewa ‘yan wannan kasuwa, sun yi asarar tumatur na kudi sama da Naira dubu 900, a lokacin da aka kafa dokar hana fita a Jihar Filato, a karon farko. A matakan da gwamnatin Jihar Filato ta dauka, na hana annobar cutar Kurona shigowa da yaduwa a jihar. Alhaji Muhammad Nasiru Sani ya bayyana haka ne, a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

  Ya ce ‘yan kasuwar  sun yi asarar tumatur da sauran  kayayyakin gwari na kudi sama da naira duba 900, a makon da ya gabata, sakamakon wannan doka ta hana fita da aka kafa a jihar.

  • Wani bangare na kasuwar ‘yan tumatur farar gada Jos…….jpg
   378.3kB

  ‘’Kwandon tumaturin da ake sayarwa kan kudi naira 1500 a wannan kasuwa, kafin a kafa wannan doka a rufe kasuwar, da aka sake bude kasuwar an samu duk sun lalace. Don haka ‘yan kasuwar suka rika sayar da Kwando naira 200, zuwa naira 300. Da dama cikin ‘yan kasuwar sun karye,  sakamakon wannan asara da suka yi’’.

  Ya yi kira ga  gwamnatin Filato  ta dubi wannan  wannan al’amari, domin ta tallafa masu.

  ‘’Kuma muna  rokon gwamnatin Filato tayi koyi da sauran gwamnonin wasu jihohin  da suka kafa dokar hana fita, amma suka bari ana shigar da kayayakin gwari, ana sayarwa da jama’a,  domin babu yadda za a yi abinci, ba tare da kayan miya  ba’’.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here