Annobar Kurona Za Ta Iya Shafar Harkokin Noma A Najeriya-Farfesa Dadari

  0
  426
  Farfesa Salihu Adamu Dadari,

  Isah Ahmed Daga  Jos

  WANI malami a sashin bincike da koyar da dabarun noma na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Salihu Adamu Dadari ya bayyana cewa babu shakka, idan annobar cutar korona ta ci gaba da yaduwu a Najeriya, zai iya shafar harkokin noma. Farfesa Salihu Adamu Dadari, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

  Ya ce tun da wannan annoba ta shafi rayuwar dan adam ne gabaki daya,  to ya shafi harkokin noma.  Don haka idan har wannan annoba ta ci gaba zuwa damina, zai shafi harkokin noma.

  Farfesa Dadari ya yi bayanin cewa hanyoyin da  annobar cutar korona, za su iya  shafar harkokin noma,  su ne ana kawo kayayyakin aikin gona kamar magunguna feshi da injinan sarrafa  noma daga kasashen waje ne.  Don haka idan wannan annoba ta ci gaba, ba za a sami damar kawo wawannan kayayyaki daga kasashen waje ba.

  Har ila yau ya ce wurare da kamfanonin  da ake daukar  kayayyakin amfanin gona, kamar masara da sauransu daga Arewacin Najeriya a kai su Legas da sauran wuraren da suke fuskantar wannan matsala ne. Don haka idan wannan matsala ta ci gaba,  ba za a sami zuwa a kai kayayyakin amfanin gonar zuwa wadannan wuraren ba. Zai zamanto masu sayarwa da masu sayen kayayyakin amfanin gonar, kowa yana jin tsoro saboda wannan matsala.

  ‘’Mafita kan wannan al’amari shi ne, mu yi imanin cewa babu wanda zai mutu kan wannan annoba, sai wanda kwanansa ya kare. Kuma mu koma ga Allah  mu ci gaba da addu’ar Allah ya yaye mana wannan annoba’’.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here