Gwamna Tambuwal Ya haramta Wa Mahaifin Mai Kamfanin Rahamaniyya Shiga Sakkwato

0
1022

Rahoton Z A Sada

GWAMNAN jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya haramta wa Alhaji Musa Bashir mahaifin mai kamfanin man fetir na Rahamaniyya shiga Sakkwato saboda cutar korona bairos.

Gwamnan Tambuwal ya shaida wa manema labarai cewa sun ji labarin daya daga cikin ‘ya’yansa gwaji ya tabbatar da yana dauke da cutar korona.

Gwamnan ya ce ya yi magana da shi har sau biyu, “amma ya nuna min yana kan hanya sai ya shigo Sakkwato, kuma na ba da umurni a mayar da shi, saboda a cikin iyalinshi akwai mai dauke da cutar Kuma shi ba a yi mashi gwaji ba.”

“Wadanda ke hulda da Alhaji Musa Bashar da ake kira Rahamaniyya su yi magana da shi kada ya kuskura ya shigo Sakkwato,” in ji Gwamna Tambuwal.

Sai dai duk da zargin da Gwamna Tambuwal ya yi bai bayar da cikakken bayani ba kan hukumar da ta tabbatar masa da cewa daya daga cikin ‘ya’yan Alhaji Musa Bashir na dauke da cutar.

Amma Gwamna Tambuwal ya ce zai dauki duk matakin da ya dace domin kare al’ummar jihar  idan har ya yi watsi da shawarar da aka ba shi.

Cutar korona na ci gaba da yaduwa a jihohin Najeriya, amma har yanzu cutar ba ta tsallaka jihar Sakkwato ba.

Tuni gwamnatin jihar ta dauki matakan dakile cutar daga jihar ta hanyar rufe iyakokinta.

Wasu al’ummar jihar kuma tuni suka fara barazana ga Alhaji Musa Bashir, kan za su dauki mataki a kansa idan har ya taka kafarsa cikin Sakkwato.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here