Harkokin Sayar Da Motoci Sun Tsaya Sakamakon Annobar Korona-Yahaya Kega

  0
  353
  Alhaji Yahaya Muhammad Kega.

  Isah Ahmed Daga Jos

  SHUGABAN kungiyar dillalan motoci ta Najeriya reshen Jihar Filato, kuma shugaban kamfanin sayar da motoci na Kega Motors Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya bayyana cewa,  sakamakon annobar cutar korona da ta game duniya yanzu, harkokin sayar da motoci sun tsaya. Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya bayyana haka ne, a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

  Ya ce dama ana cikin mawuyacin hali sakamakon halin matsin da aka shiga a kasar nan. Don haka duk da wannan cuta bata zo jihar Filato ba, amma duk wasu harkokin kasuwanci sun ja baya, da kamar kashi 60 bisa 100 musamman masu sayar da motoci.

  ‘’Kamar mu masu sayar da mota yanzu jama’a ba maganar sayen mota ake yi ba, ana maganar abincin da za a ci ne. Yanzu idan ka ga mutum ya zo wajen ka, sai dai ya kawo maka motarsa  a sayar masa. Yanzu ba a sayen mota, don jin dadi ko a da ana sayen mota ne, don biyan bukata. Don haka  da wannan annoba  ta zo, sai komai ya ja baya’’.

  Alhaji Yahaya Kega ya yaba da matakan da gwamnati take dauka, kan dakile yaduwar wannan cuta a kasar nan.

  Ya ce wadannan matakai na hana fita matakai ne masu wahalar gaske, amma gaskiya su ne maganin wannan cuta, tun da an ce babu maganin ta. Don haka ya yi kira ga  jama’a su yi biyayya da wadannan matakai, kuma su rika aiki da shawarwarin da jami’an kiwon lafiya  kan wannan annoba suke bayarwa

  Har ila yau ya yi kira ga jama’a a cigaba da addu’ar  Allah ya fitar da mu, daga wannan bala’i da muka shiga.

  Ya yi kira ga gwamnati ta tallafa wa jama’a, domin maganar ka hana mutum fita ya nemi abinci, abu ne mai matukar wahala.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here